Hausa
Surah Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya count 36
وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ
( 1 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 1 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 1](style/islamic/icons/mp3.png)
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُوا عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ
( 2 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 2 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 2](style/islamic/icons/mp3.png)
Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ
( 3 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 3 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 3](style/islamic/icons/mp3.png)
Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
أَلَا يَظُنُّ أُولَٰئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ
( 4 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 4 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 4](style/islamic/icons/mp3.png)
Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
لِيَوْمٍ عَظِيمٍ
( 5 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 5 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 5](style/islamic/icons/mp3.png)
Domin yini mai girma.
يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ
( 6 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 6 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 6](style/islamic/icons/mp3.png)
Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ
( 7 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 7 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 7](style/islamic/icons/mp3.png)
Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌ
( 8 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 8 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 8](style/islamic/icons/mp3.png)
Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ
( 9 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 9 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 9](style/islamic/icons/mp3.png)
Wani 1ittãfi ne rubũtacce.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 10 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 10 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 10](style/islamic/icons/mp3.png)
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ
( 11 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 11 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 11](style/islamic/icons/mp3.png)
Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ
( 12 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 12 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 12](style/islamic/icons/mp3.png)
Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ
( 13 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 13 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 13](style/islamic/icons/mp3.png)
Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
كَلَّا ۖ بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ
( 14 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 14 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 14](style/islamic/icons/mp3.png)
A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
كَلَّا إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ
( 15 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 15 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 15](style/islamic/icons/mp3.png)
A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُو الْجَحِيمِ
( 16 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 16 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 16](style/islamic/icons/mp3.png)
Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ
( 17 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 17 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 17](style/islamic/icons/mp3.png)
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ
( 18 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 18 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 18](style/islamic/icons/mp3.png)
A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَ
( 19 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 19 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 19](style/islamic/icons/mp3.png)
Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ
( 20 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 20 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 20](style/islamic/icons/mp3.png)
Wani littãfi ne rubũtacce.
يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَ
( 21 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 21 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 21](style/islamic/icons/mp3.png)
Muƙarrabai suke halarta shi.
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ
( 22 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 22 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 22](style/islamic/icons/mp3.png)
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ
( 23 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 23 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 23](style/islamic/icons/mp3.png)
A kan karagu, suna ta kallo.
تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِ
( 24 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 24 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 24](style/islamic/icons/mp3.png)
Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ
( 25 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 25 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 25](style/islamic/icons/mp3.png)
Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
خِتَامُهُ مِسْكٌ ۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ
( 26 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 26 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 26](style/islamic/icons/mp3.png)
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
وَمِزَاجُهُ مِن تَسْنِيمٍ
( 27 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 27 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 27](style/islamic/icons/mp3.png)
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ
( 28 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 28 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 28](style/islamic/icons/mp3.png)
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُوا مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَ
( 29 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 29 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 29](style/islamic/icons/mp3.png)
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
وَإِذَا مَرُّوا بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ
( 30 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 30 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 30](style/islamic/icons/mp3.png)
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
وَإِذَا انقَلَبُوا إِلَىٰ أَهْلِهِمُ انقَلَبُوا فَكِهِينَ
( 31 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 31 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 31](style/islamic/icons/mp3.png)
Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَضَالُّونَ
( 32 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 32 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 32](style/islamic/icons/mp3.png)
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ
( 33 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 33 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 33](style/islamic/icons/mp3.png)
Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُوا مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ
( 34 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 34 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 34](style/islamic/icons/mp3.png)
To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ
( 35 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 35 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 35](style/islamic/icons/mp3.png)
A kan karagu, suna ta kallo.
هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ
( 36 ) ![Hausa - Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 36 Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) - Aya 36](style/islamic/icons/mp3.png)
Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?